Tunisia ta fitar da kasar Ghana a bugun daga kai sai mai tsaron raga wanda hakan ya bata damar kaiwa zagayen kusa da na karshe
Alhamis, Yuli 11, 2019
Tunisia ta fitar da kasar Ghana a bugun daga kai sai mai tsaron raga  wanda hakan ya bata damar kaiwa zagayen kusa da na karshe

Kungiyar kwallon kafa ta kasar Tunisia ta samu nasar akan takwararta ta kasar Ghana a bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan sunyi kunnen doki da ci daya da daya a wasan da suka buga a yammacin yau a filin wasa na Isma'iliyya a zagayen kungiyoyi sha shida na gasar cin kofin kwallon kafa na kasashen Afirka 2019.

- Da wannan sakamako ne kungiyar kwallon kafa ta kasar Tunisia zata kara da takwararta ta kasar Madagascar a zagaye na kusa da na karshe da misalin karfe tara na yammacin Alhamis mai zuwa a filin wasa na Salam.