Nigeria ta tarar da kasar Senegal a zagayen wasan kusa da karshe na kofin kasashen Afirka bayan ta samu nasara akan kasar Afirka ta kudu
Laraba, Yuli 10, 2019
Nigeria ta tarar da kasar Senegal a zagayen wasan kusa da karshe na kofin kasashen Afirka  bayan ta samu nasara akan kasar Afirka ta kudu

 Kungiyar kwallon kafa ta Nigeria ta nasarar samun tikitin zuwa wasan kusa da karshe, bayan ta doke kasar Afirka ta kudu da ci biyu da daya (2 - 1) a ranar laraba a filin wasa na Alk'ahira a cikin wasannin zagayen kusa da na karshe. ana gab da za'a tashi daga wasan a daidai minti na 90, William Ekong ya samu nasarar zura kwallo bayan mai tsaron raga na Afirka ta kudu ya yi kuskuren fitowa, haka wasan ya kare Nigeria ta yi nasara da ci 2- 1.

Kungiyar kwallon kafa ta Nigeria tana jiran wanda zai yi nasara tsakanin Algeria da kasar Cote d'Ivoire a wasan kusa da karshe.