Kofin Nahiyar Afirka: Nijeriya Za Ta Fafata Da Kamaru A Zagaye Na Biyu
Talata, Yuli 02, 2019
Kofin Nahiyar Afirka: Nijeriya Za Ta Fafata Da Kamaru A Zagaye Na Biyu

Nijeriya za ta fafata da kasar kamaru a zagaye na biyu a gasar kofin nahiyar Afrika. Kamaru wadda ke rike da kofin a halin yanzu ta tashi daga wasan da ta buga yau Talata da Benin ba tare da an gefa kwallo ko daya ba wanda hakan ya baiwa kasar Ghana damar karewa a matsayi na daya a rukunin F. Wannan shine karo na biyu da Kamuru da doka wasa kuma aka tashi ba tare da an jefa kwallo ko daya a raga a wannan gasar. Nigeriya ta kare a matsayi na biyu a rukunin B bayan tayi rashin nasara a hannun Madagascar Za’a buga wasan ranar Asabar 6 ga watan Yuli da misalin karfe 5:00 na yamma.

Source: leadership a yau