AFCON: Najeriya za ta fafata da Kamaru
Talata, Yuli 02, 2019
AFCON: Najeriya za ta fafata da Kamaru

Super Eagles za ta kara da babbar abokiyar hamayyarta Kamaru a zagaye na biyu na gasar cin kofin kasashen Afirka da ake yi a Masar.

Kamaru ta kai wannan mataki ne bayan da ta tashi canjaras da Benin a rukunin F, inda ta zo ta biyu da maki biyar bayan Ghana.

Ita kuwa Najeriya ta kasance ta biyu anata rukunin ne bayan da ta sha kaye a hannun Madagascar da ci 2-0

Ana sa ran wasan zai ja hankali sosai ganin yadda kasashen biyu suka dade suna hamayya da juna a fagen kwallon kafa.

Source: bbc